<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>308</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Sunan wani yaro fa, Daniel ke nan,
 An haife shi cikin Yahudiya wata ran.
 Cikin zamaninsa, Allah ne ya sa
 Mutanensa su horu a ƙasar magauta.

[V2]
 KORUS
 Tsoron Ubangiji farkon ilmi ne,
 Sai mu tsaya kamar yadda Daniel ya yi.

[V3]
 2) Cikin aikin sarki dai, ya yi aminci.
 Aka gabatad da shi ya zama sananne.
 Cikin wannan duka, shaida ya ke yi,
 Ba ya neman girman kansa, sai na Allahnsa.
 Korus

[V4]
 3) Zancen yin addu'arsa, ba ya fasawa,
 Kunya ba ya taƃa ji a cikin wannan ba.
 Can fa wata ra na a ke ƙararsa,
 Duk da haka ya yi ta addu'a kamar da.
 Korus

[V5]
 4) Cikin ramin zakuna aka jefa shi,
 Ba su iya buɗe baki ba, balle su ci.
 Daniel ya kwana lafiya ƙalau,
 Can da safe ya ji  muryar sarki, cewa &quot;Zo&quot;
 Korus

[V6]
 5) Ikon Ubangijinmu ba ya kasawa.
 Har yanzu akwai shi isasshe ne dominka
 Kada ka yi shakka, ko ka ji tsoro
 Wurin Ubangiji dukan kome ya yiwu.</lyrics>
<title>Sunan Wani Yaro Fa, Daniel Ke Nan LW308</title>
</song>